Nigeriya ta ce za ta nemi hanyar karfafa huldar al'adu da kasar Sin musamman a bangaren yawon shakatawa, kamar yadda ministan yada labarai, al'adu da yawon shakatawan kasar Lai Mohammed ya sanar a Talatan nan a Abuja.
Da yake magana a ganawar sa da jakadar kasar Sin a Nigeriya Gu Xiaojie, ministan ya ce, a lokacin aikin sa a wannan ofishi, zai tabbatar da kasashen biyu su karfafa hadin gwiwwar da yanzu hakan suke da shi a bangaren yawon shakatawa.
Ya ce, Sin kasa ce mai ci gaba da ta dace wajen hadin gwiwwa da Nigeriya. Ya lura da zumuncin dake tsakanin kasashen biyu ya fara ne daga matakin al'adu, amma yanzu har ya wuce hakan zuwa matakin ayyukan ci gaba.
Ministan wanda ya kuma amsa gayyatar ofishin jakadancin da ya halarci babban taron na duniya na farko a kan yawon shakatawa da za'a yi a watan Mayun wannan shekarar a kasar Sin, ya ce, ziyarar za ta ba shi damar musanyar ra'ayi da mahukuntar kasar Sin a kan yadda za'a taimaka a inganta bangaren yawon shakatawa a Nigeriya.
Tun da farko a jawabin shi jakadan kasar Sin a Nigeriyan Gu Xiaojei, ya bayyana zumuncin dake tsakanin kasashen biyu a matsayin abin sha'awa mai kunshe da dabaru, yana mai lura cewa, bangarorin biyu suna zumuncin na moriyar juna cikin shekaru 45 da suka yi na hadin gwiwwa.(Fatimah)