Domin taimakawa kasar Saliyo wajen yaki da cutar Ebola, a watan Satumba na shekarar 2014, aka canja asibitin sada zumunta tsakanin kasashen Sin da Saliyo zuwa cibiyar kula da masu fama da cutar Ebola, Kuma ayarin likitocin da Sin ta tura don yaki da cutar Ebola sun ba da babbar gudammawa wajen yaki da cutar Ebola a kasar.
Ganin yanzu an kusan cimma nasarar yaki da cutar Ebola, bisa bukatu daga gwamnatin Saliyo, Sin ta gyara wannan asibiti domin bude kofa ga marasa lafiya na yau da kullum. A ranar 4 ga watan Agustar nan ne bayan da aka kashe kwayoyin cuta da gudanar da gyare-gyare, aka sake bude asibitin sada zumunta tsakanin kasashen Sin da Saliyo. Kwararrun da Sin ta tura zuwa Saliyo su 9, da nas nas na kasar ta Saliyo 30 sun fara gudanar da aiki a asibitin. (Bako)




