in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kwamitin tsakiya na JKS ya fidda muhimmiyar takarda game da aikin gona
2016-01-27 21:02:46 cri

Kwamitin tsakiya na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin, ya gabatar da muhimmiyar takarda, wadda ke da nufin raya ayyukan gona da kauyuka gami da manoma.

Takardar ta bayyana cewa, a sabon yanayin da ake ciki na raya tattalin arziki, da tsimin makamashi, akwai wasu manyan batutuwa da tilas ne a warware su game da aikin gona, da raya kauyuka, ciki hadda kara yawan kudin shigar manoma cikin sauri, don tabbatar da dukkanin al'umma su samu wadata kamar yadda aka shirya. Kaza lika akwai bukatar saita hanyar raya sha'anin noma, don tabbatar da samun isashen hatsi da amfanin gona, gami da kara karfin takara a fannin aikin gona a kasuwannin duniya. (Amina)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China