Lu Kang ya ce, a ranar 18 ga watan Nuwamba na shekarar bana, Ursula Gauthier ta samar da wani rahoto a mujallar Le Nouvel Observateur ta kasar Faransa, inda ta nuna goyon baya ga wadanda suka aikata lafuffukan ta'addanci da kuma kashe fararen hula, lamarin da ya tada hankulan jama'ar kasar Sin sosai, shi ya sa a ganin kasar Sin, bai dace da ta ci gaba da yin aiki a nan kasar ba, haka kuma, ya kamata ta nema gafara daga jama'ar kasa ta Sin kan wannan batu.
Bugu da kari, ya ce, a kullum, kasar Sin tana kiyaye ikon kamfanonin dillancin labarai na kasashen waje dake nan kasar Sin da kuma 'yan jaridun su a kasar yadda ya kamata, amma ba za ta lamunci wani ya goyi baya ta'addanci a kasar ba. (Maryam)