in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Najeriya za ta warware matsalar faduwar darajar kudi a shekara mai zuwa
2015-12-21 10:47:29 cri

Gwamnan babban bankin Najeriya CBN Godwin Emefeile, ya ce, mahukuntan kasar na daukar karin matakai, na bunkasa tattalin arziki da daidaita darajar kudin kasar Naira. Sai dai bai bayyana irin matakan da za a dauka ba.

Mr. Emefeile, ya bayyana hakan ne a birnin Abuja, fadar mulkin kasar, yana mai cewa, tattalin arzikin Najeriyar, bai yi tabarbarewar da ake zato ba, idan aka kwatanta da na wasu kasashen nahiyar Afirka.

Kaza lika ya yi kira ga 'yan kasuwa dake shigo da hajojin su daga ketare, da su mai da hankali ga sayo kayan da ake iya sarrafawa, maimakon wadanda aka gama sarrafa su, da kayayyakin abinci. Hakan a cewar sa zai rage matsin lambar da kudin kasar ke fuskanta a fannin canji kudaden waje.

Gwamnan bankin na CBN ya kara da cewa, daya daga cikin hanyoyin dakile faduwar darajar kudin Naira shi ne, ta hanyar daidaita bukatar da ake da ita ga kudaden waje kamar dalar Amurka. Ya kuma zargi wasu marasa kishin kasar da gudanar da hada-hada, wadda ke dada karya darajar Naira a kan dalar Amurka, da ma sauran kudaden kasashen waje.

Kaza lika, Emefiele ya ce, dole ne Najeriya ta komawa noma domin samarwa kan ta abincin da take bukata.

A cewarsa, babban bankin Najeriya ya samar da kyakkyawan yanayi, na bunkasar kanana da matsakaitan masana'antu, ta hanyar samar da lamuni mai sauki ga masu bukata.

Daga nan sai ya bukaci 'yan Najeriya da su kara hakuri da irin matakan da gwamnati mai ci ke dauka, na ganin ta shawo kan matsalolin dake addabar kasar, da ma mawuyacin halin da al'ummar ta ke ciki.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China