Ministan harkokin cikin gidan Tarayyar Najeriya Abdulrahman Dambazau, ya jinjinawa irin kyakkyawar dangantakar dake tsakanin Najeriya da kasar Sin, yana mai cewa akwai bukatar karfafa hadin gwiwar sassan biyu ta yadda za su ci gaba da cin gajiyar kawancen su.
Dambazau ya bayyana hakan ne yayin ganawar sa da jakadan kasar Sin a Najeirya Gu Xiaojie a Abuja, fadar mulkin Najeriya. Kaza lika ministan ya bada tabbacin tsaro da kyakkyawan yanayi ga masu zuba jari a Najeriya daga kasar ta Sin, yana mai cewa gwamnatin Najeriya na daukar karin matakan inganta tsaron lafiya da dukiyoyin al'umma yadda ya kamata.
Kafin hakan a nasa tsokaci, Mr. Gu ya ce Sin na da burin zuba jari a kusan daukacin sassan tattalin arzikin Najeriya, a yunkurinta na bunkasa ci gaban kasashen biyu.(Saminu Alhassan)