Shugaban kasar Kenya Uhuru Kenyatta, a ranar Litinin din nan ya bukaci a gudanar da harkokin kasuwanci na daidai wa daida a tsakanin kasashen duniya, sannan ya bukaci ministoci mahalarta taron WTO wanda za'a gudanar a Nairobi, tun daga yau Talata da su janye tallafin a fannin aikin gona ga kasashen duniya mafiya arziki.
Da yake jawabi a yayin taron musayar ra'ayoyi na kasar Sin karo na hudu a Nairobi, Kenyata ya ce, ya kamata dokokin cikiniyya a fannin aikin gona su kasance babu nuna fifiko, ya kara da cewa, dokokin da kasashen yammacin duniya suka sanya da sunan tallafi, suna matukar yin illa ga kasashen Afrika, musamman a fannin aikin gona da harkokin masana'antu.
Ya ce, idan har ana son ci gaba ta fuskar masana'antu, to ya zama tilas a cire kudaden haraji masu tsanani.
Ya kara da cewar, an kafa WTO ne da nufin kawar da duk wani batu na nuna wariya a dokokin da suka shafi harkar cikikayya ta duniya, da bude kofa ga ko wace kasa, da gudanar da harkokin cinikayya a bude, da kuma mutunta dokokin da suka shafi tattalin arziki na kasashen duniya baki daya.
Kenyatta ya ce, yana fatan wannan taron tattaunawa na kasar Sin, zai yi tasiri wajen cimma jarjejeniyar kasuwanci, ta yadda kasashen duniya za su samu damar fitar da kayyyakin da suke samarwa ba tare da nuna tsangwama ba, kuma ana fatan hakan zai yi sanadiyyar samar da guraben aiki ga matasa a fannin hada hadar kasuwanci.
Shugaba Kenyatta ya ce, ya lura taron tattaunawa na kasar Sin karo na 4, wanda shi ne ya jagoranci budewa a Nairobi, wata dama ce da za ta karfafa matsayin dokokin da suka shafi kasuwanci tsakanin kasashen duniya.
Shugaban ya bukaci taron na WTO da ya mayar da hankali wajen sauke nauyin da yake wuyansa wajen aiwtar da abubuwan da suka dace, ya kara da cewar, babu yadda za'a yi a samu ci gaban tattalin arziki ba tare da yin hulda da juna ba.(Ahmad Fagam)