Mutum guda ya rasu, sannan wasu 20 sun jikkata a sakamakon firgita da suka yi, a yayin aiwatar da gwajin tunkarar hare haren ta'addanci a ranar Litinin din nan a jami'ar kasar Kenya dake birnin Nairobi.
Esther Kidambi, mai shekaru 33 kuma ma'aikaciya ce a jami'ar ta Strathmore, ta cika a gadon asibiti na jami'ar a sakamakon samun munanan raunuka.
Kafin rai ya yi halinsa, marigayiyar ta ce, ta tsallako daga hawa 3 ne lokacin da ta ji karar harbe harbe.
Duk wani kokarin da aka yi na ceto rayuwarta ya ci tura, kamar yadda sanarwar da jami'ar ta fitar.
Jami'an tsaro na jami'ar ta Strathmore ne suka gudanar da gwajin, sai dai wasu dalibai da ma'aikatan jami'ar sun ce ba'a sanar da su ba kafin gwajin.
Jami'an tsaron jami'ar sun yi ta barin wuta a lokacin gwajin, lamarin da ya haddasa tsoro da firgici a zukatan jama'a a cikin jami'ar.
Wasu dalibai da wani farfesa sun diro daga wasu dogayen gini, kuma sun samu raunuka yayin da suke zaton harin ta'addacin ne aka kai jami'ar, kuma 4 daga cikin wadanda suka jikkata na cikin mawuyacin hali a gadon asibiti, amma ana ci gaba da duba lafiyarsu.(Ahmad Fagam)