in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Afrika ta Kudu za ta koyi da tsarin Sin domin bunkasa masana'antunta
2015-07-13 09:51:43 cri

Kasar Afrika ta Kudu za ta koyi da tsarin kasar Sin a cikin shirinta na bunkasa masana'antu, in ji fadar shugaban kasar a ranar Lahadi.

Wannan shi ne daya daga cikin makasudan ziyarar da mataimakin shugaban kasar Cyril Ramaphosa zai kai a kasar Sin, daga ranar 13 zuwa 17 ga watan Juli, in ji kakakinsa Ronnie Mamoepa. Ziyarar za ta mai da hankali kan batutuwan tattalin arziki da kasuwanci, musamman ma kan rawar da kamfanonin gwamnati ke takawa ga bunkasuwar tattalin arziki, kawar da talauci, da yaki da zaman kashe wando, in ji Mamoepa.

A yayin wannan rangadi a kasar Sin, mista Ramaphosa zai gana da shugaban kasar Sin Xi Jinping, da kuma faraminista Li Keqiang. Haka kuma zai samu ganawa tare da takwaransa na kasar Sin Li Yuanchao domin tattauna wasu batutuwan da ke da nasaba da shirin dabaru na shekaru biyar zuwa goma, da aka sanya hannu a yayin ziyarar shugaban kasar Afrika ta Kudu Jacob Zuma a kasar Sin a shekarar bara, in ji Mampoepa.

A cewar kakakin, shawarwarin za su tabo dangantakar kasuwanci, zuba jari, kudi, gine ginen ababen more rayuwar jama'a, makamashi, ilimi da batun dandalin dangantaka tsakanin Sin da Afrika mai zuwa da za a shirya a karshen wannan shekara a Afrika ta Kudu.

A halin yanzu kasar Sin ita ce babbar abokiyar huldar kasuwanci ta Afrika ta Kudu, kuma adadin musanyar kasuwanci tsakanin kasashen biyu ya tashi daga dalar Amurka biliyan 9,52 a shekarar 2009 zuwa biliyan 22 a shekarar 2013. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China