in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Benin ta cimma wani shirin kasa na yaki da cutar Sida da saura cututtukan jama'i masu yaduwa
2015-12-02 10:27:49 cri

Gwamnatin kasar Benin ta amince da wani shirin kasa na yaki da cutar kanjamau da sauran cututtukan jama'i masu yaduwa bisa lokacin shekarar 2015 zuwa 2017, in ji Pascal Togbé, ministan kiwon lafiyar kasar Benin a birnin Cotonou a ranar Talata.

Shirin kasa na yaki da cutar Sida ya kasance wata hanyar misali ga duk wasu ayyukan yaki da Sida, kamar tsarin "Three Ones", daukar nauyi, tsarawa da daidaitawa, na kulawar dake dogaro da sakamakon aka amince, in ji ministan.

Ya kuma nuna cewa, wannan shiri zai karfafa sakamakon da aka samu ta amsar kasa kan HIV da Sida, da kuma aiwatar yadda ya kamata da matakan dake da nasaba da samar da magungunan kashe kaifin cutar Sida kyauta, gwajin jini da bincikin lafiya zuwa ga 'yan kasar Benin dake rayuwa da cutar Sida.

A cewar jami'in, wannan shiri ya rataya kan matakai hudu, wanda mataki na farko ya shafi karfafa yin rigakafi kan yaduwar cutar Sida da sauran cututtukan jama'i, bisa manufar rage da kashi 30 cikin 100 sabbin masu kamuwa da wannan cuta kafin shekarar 2017.

Mataki na biyu, mai da hankali kan hana yaduwar cutar Sida daga uwa zuwa da, bisa manufar rage da kashi 75 cikin 100 kafin shekarar 2017, sabbin masu kamuwa da cutar daga yaran da suka fi zama cikin hadari, har ma da kawar da mace macen da ake dangantawa da HIV a wajen kananan yara masu watanni 18 da haifuwa.

Mataki na uku, ya shafi daukar nauyin mutanen dake rayuwa da cutar HIV da kuma marayu da yaran dake cikin hadari, wanda zai ba da damar rage da kashi 50 cikin 100 kafin shekarar 2017, yawan mutuwar mutanen dake dauka da cutar, har ma kuma da rage da kashi 70 cikin 100 yawan marayu da yaran dake cikin hadari.

Kana mataki na hudu, a cewar mista Pascal Togbé, ya rataya kan amsar gwamnati na sanya ido da kimantawa tare da karfafa tsare-tsare, wanda zai taimaka wajen karfafa shiryawa, tsarawa da kuma aikin hukuma. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China