Ministan harkokin wajen Rasha Sergei Lavrov ya fada a ranar Talata cewar, Rasha da Amurka za su hada kai don yin aiki tare, da nufin kawo karshen rikicin Syria, duk kuwa da irin bambamce bambamcen dake tsakanin kasashen biyu.
Lavrov, ya ce, an samu gagarumin ci gaba a tattaunawar da aka gudanar a ranar Litinin da ta gabata tsakanin shugaba Vladimir Putin na Rasha da takwaransa na Amurka Barrak Obama.
Shugabannin biyu sun gana ne a yayin babban taron MDD, kuma tattaunawar tasu ta tsawon mintuna 100 ta mai da hankali ne kan yaki da ta'addanci a yankin Gabas ta Tsakiya, musamman ma a kasar Syria.
Shugabannin biyu dai, sun cimma matsaya guda na kokarin dakile aniyar kungiyar IS mai fafutukar kafa daular Islama, shugabannin na Rasha da Amurka sun lashi takobin murkushe kungiyar ta IS, da hana ta cimma burinta.(Ahmad Fagam)