An gano wasu gawawwakin mayakan kungiyar Boko Haram biyar tare da wasu makaman harba roka a ranar Lahadi da safe, inda suka sanya wuta a wata makaranta, kuma suka kai wani harin gurmeti a gidan wani sarki a cikin dare a Afade, wani kauyen a yankin arewa mai nisa na Kamaru dake kusa da iyaka da Najeriya, a cewar majiyoyin tsaro.
Wani gungun mutane dauke da makamai fiye da goma ne suka kai harin a kan babura, an zarge su mayakan kungiyar Boko Haram ta Najeriya ne, kuma jami'an tsaron kasar Kamaru suna kokarin murkushe su a wannan yankin arewa mai nisa. (Maman Ada)