Jami'an tsaro sun tabbatar wa kamfanin dillancin labaran kasar Sin Xinhua cewar, a kalla mutane 8 ne suka mutu a ranar Lahadin nan a sakamakon wani harin kunar bakin wake a yankin Sangueleri dake arewacin kasar Kamaru a kusa da iyakar Kamarun da Najeriya.
A cewar majiyar, wata mata 'yar kimanin shekaru 25 ne ta tada bom din dake jikinta da misalin karfe 8 na safe, kuma nan take bom din ya hallaka ta da saura mutane 7, yayin da wasu mutane 6 suka samu raunuka.
Wannan shi ne hari na 14 a jerin hare haren da aka kai a arewacin Kamaru daga farkon watan Yunin wannan shekara.
Ko da yake babu wata kungiya da ta dauki nauyin kai harin, amma jami'an tsaro na zargin kungiyar Boko Haram da ta kai harin.(Ahmad Fagam)