Shi dai wannan mutumin ya taba yin mu'amala da wani mutum da aka tabbatar ya kamu da cutar Ebola a cikin watan Ramadan. Bayan da ya nuna alamar kamuwa da cutar Ebola ne, aka kai shi wata cibiyar bada jinya ga wadanda suka kamu da cutar Ebola dake arewacin kasar. Kuma yanzu haka ya samu sauki, an kuma sallame shi daga asibiti.
Shugaban kasar Saliyo Ernest Bai Koroma ya halarci bikin sallamar tasa daga asibitin, inda ya sanar da cewa, bisa ma'aunin kawo karshen cutar Ebola da hukumar kiwon lafiya ta duniya wato WHO ta tsara, tun daga ranar 25 ga watan Agusta, kasar Saliyo za ta fara kidaya kwanakin da aka tsara wato kwanaki 42 na ganin babu wanda aka samu yana dauke da cutar.
Amma shugaba Koroma ya gargadi jama'ar kasar cewa, koda yake kasar Saliyo ta shiga wannan muhimmin lokaci tun bayan da cutar Ebola ta barke a kasar har na tsawon kwanaki 486, ya kamata jama'a su kara yin taka tsantsan na kiyaye lafiyarsu don magance sake kamuwa da cutar Ebola. (Zainab)




