Shugaban kasar Somaliya, Hassan Sheikh Mohamoud ya yi kashedi a ranar Laraba ga mayakan kungiyar Al-Shabaab kan duk wata mubaya'a da wasu kungiyoyin ta'addanci domin tsaurara hare-harensu kan gwamnatin Somaliya da kasashen yammacin duniya suke goyon baya.
Mista Mohamoud ya yi kira ga masu kaifin kishin islaman da su zabi kai kansu maimakon yin mubaya'a da wata kungiyar Al-Qaida ko kungiyar IS.
Muna mai da hankali sosai kan muhawarar da za a iya cewa ta bainar jama'a a cikin kungiyar Al-Shabaab, domin sanin ko za su yi mubaya'a ga kungiyar Al-Qaida, ko kuma ga kungiyar IS, kamar yadda ya kamata a kira su "masu kashewa ko masu lalatawa", in ji mista Mohamoud, a cikin wata sanarwa da aka fitar a birnin Mogadishu. (Maman Ada)