Hukumar 'yan sanda a kasar Somaliya ta ce, a ranar Lahadin nan ta kama wasu mutane da ake zargin mayakan kungiyar Al-Shabaab ne, sannan ta samu nasarar kwace makamai masu yawa daga hannunsu a lokacin wani sumame da jami'an 'yan sandan suka kai a wani garin dake kudancin kasar.
A cewar wani babban jami'i a hukumar 'yan sandan kasar Abdiqani Shu'ayb, hukumar 'yan sandan ta yi amanna cewar, mutanen da ta kama suna da alaka da kungiyar Al-Shabaab, kuma ta gano wani yunkurin kai hari da mayakan ke yi a garin Bardere na yankin Gedo wanda a kwanan nan dakarun kasar suka kwato shi daga hannun mayakan na Al-Shabaab.
Shu'ayb ya sheda wa kamfanin dillancin labaran kasar Sin Xinhua cewar, wasu bayanan sirri da hukumar 'yan sandar kasar ta tattara sun gano wani yunkuri da mayakan na Al-Shabaab ke yi da nufin afkawa garin Bardere, don wargaza zaman lafiyar yankin, ya kara da cewar, ba za su yi kasa a gwiwa ba wajen fafutukar tabbatar da tsaro a kasar.
A farkon wannan wata ne dai, dakarun gwamnatin kasar Somaliya da hadin gwiwar sojojin wanzar da zaman lafiya na kungiyar hada kan Afrika wato AU suka kwace ikon garin na Bardera, suka fatattaki mayakan na Al-Shabaab daga garin.(Ahmad Fagam)