Sakamakon wani bincike da MDD ta gudanar game da kasar Somaliya, ya nuna cewa, yawan al'ummar kasar dake fama da karancin abinci, shekaru 4 bayan aukuwar fari ya yi matukar karuwa da kashi 17 cikin dari, adadin da ya haura mutane 850,000.
A cewar jami'in MDDr mai lura da ayyukan jin kai a kasar ta Somaliya Peter de Clercq, al'ummar kasar na cikin halin matukar matsi game da rashin abinci, da karancin abinci mai gina jiki, don haka ya zama wajibi masu ruwa da tsaki su tashi tsaye wajen kare kazantar halin da ake ciki. Clercq ya kara da cewa, halin kamfar abinci a Somaliya ya fi tsananta tsakanin al'ummun da suka rasa matsugunnansu
A shekarar 2011 ne Somaliya ta fuskanci matsanancin fari, kuma kasar ta fara farfadowa daga wannan bala'I, a cewar hukumar kula da ayyukan jin kai ko OCHA, ko da yake har ya zuwa yanzu akwai 'yan kasar kusan miliyan 3 dake bukatar tallafi, musamman ma idan aka yi duba da raunin kasar wajen jure bala'u. (Saminu)