in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Dakarun Somaliya da AU sun kashe masu tada kayar baya 17 a kudancin kasar
2015-07-23 10:52:37 cri

Dakarun kungiyar tarayyar Afrika (AU) da na kasar Somaliya sun kashe masu tada kayar baya goma sha bakwai a ranar Laraba a cikin wani gumurzu da kungiyar Al-Shabaab a wasu kauyuka da dama dake yankin Bakol, a kudancin kasar Somaliya.

Aden Abdi, mataimakin magajin garin Hudur, a yankin Bakol, ya bayyana cewa, sun karbe ikon wasu karkara uku kusa da Hudur a cikin wani bata kashi, tare da kashe mayakan kungiyar Al-Shabaab goma sha bakwai.

Haka kuma mista Abdi ya nuna cewa, yanzu mayakan Al-Shabaab sun mai da sansaninsu a kauyen Fijo dake yankin Bakol, tuni kuma dakarun hadin gwiwa suna kan hanyar zuwa kauyen domin murkushe 'yan ta'addan.

Dakarun gwamnatin Somaliya da na kungiyar tarayyar Afrika (AU) sun kaddamar da wani babban aikin kakkabe sansanonin kungiyar Al-Shabaab da suka rage a yankunan Bakol, Bay da Gedo dake kudancin Somaliya domin kawar da mayakan daga wurarensu.

Dakarun hadin gwiwa sun karbe ikon birnin Bardere, sansanin kungiyar Al-Shabaab na baya bayan nan, wanda ya kasance muhimmin wuri da mayakan ke amfani da shi wajen kaddamar da hare harensu na ta'addanci. Birnin da tsaya kan ikon kungiyar Al-Shabaab har na tsawon shekaru biyar. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China