A game da hakan Sin tace ya zama dole Amurka ta dakile tunanin yakin cacar baka, ta bi daidaito da aka cimma tsakanin shugabannin kasashen biyu, don ci gaba da kokarta wajen kafa sabon nau'in dangantakar dake tsakanin kasashen biyu.
Kakakin ma'aikatar harkokin wajen Sin Madam Hua Chunying ta bayyana hakan a yau Jumma'a 3 ga wata lokacin da take amsa tambayoyin manema labaru game da wannan sabon rahoto kan manyan tsare-tsare a fannin soji na kasar da Amurka ta fidda.
Madam Hua ta ce, a kwanan baya, sojojin Amurka sun fidda rahoto kan manyan tsare-tsaren soji na kasar na shekarar 2015, inda aka nuna cewa, Amurka za ta ci gaba da inganta hakikanin hadin gwiwa game da harkokin soji da kasar Sin, amma a dayan hannu, ta ce, aikin gine-gine da Sin ta yi a tsibiran kudancin teku na kasar ya kawo halin kunci a yankin Asiya da tekun Fasific.(Bako)