in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Rundunar tsaron Somaliya ta kai harin sama domin shugabannin Al-Shabaab
2015-06-23 09:46:20 cri

A ranar Litinin din nan rundunar tsaron kasar Somaliya ta tabbatar da cewar, ta kai harin sama a daren ranar Lahadi da nufin samun shugabannin kungiyar 'yan ta'adda ta Al-Shabaab.

Kamar yadda kakakin ma'aikatar harkokin cikin gida Mohammed Yusuf ya tabbatar, rundunar tsaron daga hukumar leken asiri ta kasar ta kai harin saman ne a Bardhere dake gundumar Gedo, inda shugabannin Al-Shabaab din suke aiwatar da taro.

Mohammed Yusuf ya ce, an shirya wannan harin kuma yana daga cikin ayyukan tsaron da za'a aiwatar a cikin 'yan kwanakin nan masu zuwa a kan kungiyar 'yan ta'addan a kasar, yana mai tabbatar da cewa, bayan harin da suka kai sojojin kasar sun koma sansaninsu lami lafiya.

Sai dai kakakin bai tabbatar da cewa, ko an yi nasarar kashe jagoran kungiyar Aden, da kuma adadin mayakan da suka hallaka a harin.

Wannan harin saman dai ya zo ne kwana daya bayan da kungiyar Al-Shabaab ta kaddamar da mummunan harin ramuwar gayya a kan cibiyar horon jami''an leken asiri kusa da cibiyar hukumar leken asirin dake Mogadishu, abin da ya yi sanadiyar mutuwar mayakan guda 4. (Fatimah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China