Wani rahoton hadin gwiwa tsakanin kungiyar kiwon lafiya ta duniya (WHO) da asusun kula da yara kanana na MDD (UNICEF), ya nuna cewa, Ghana ita ce kasa ta bakwai a cikin jerin kasashen duniya ta fuskar rashin ingancin tsarin kiwon lafiya, a cewar kafofin kasar a ranar Laraba a birnin Accra.
Wannan sabon rahoto da aka fitar a ranar Talata ya bayyana karara cewa, wahalhalun samun tsarin kiwon lafiya mai inganci sun ci gaba da tabarbarewa a kasar Ghana, kana kuma kasar ta kara ja da baya bisa wannan takardan fidda gwani, inda ta fado zuwa kasa ta bakwai wato matsayi mafi muni a jerin kasashen duniya. Wannan rahoto ya kasance dai wani sakamakon aikin hadin gwiwa tsakanin WHO da UNICEF. (Maman Ada)