Ministan cinikayya da masana'antun kasar Ghana Ekwow Spio Garbrah, ya yi kira ga masu zuba jari daga kasar Sin, da su mai da hankali ga fannin masana'antun kasarsa, domin ba da gudummawa wajen raya tattalin arziki.
Mr. Garbrah, wanda ya gabatar da wannan kira yayin ziyarar da ya kaiwa jakadan kasar Sin dake kasar ta Ghana Sun Baohong, ya kara da cewa, a akwai babbar dama ta samun riba a fannin masana'antun sarrafa amfanin gona, da na kere-kere wadanda za su amfani kasar yadda ya kamata.
Ya ce, akwai bukatar masu zuba jari Sinawa su yi amfani da damar albarkatun kasa da Ghana ke da su, ta yadda za su taimaka wajen fadada moriyar kasar, duba da yadda Sin ke da kwarewa a fannin fasahohin zamani, da dabarun ci gaba, wadanda za su taimaka wajen cimma burin da aka sanya gaba.
Yayin zantawar tasu, jami'an biyu sun kuma tattauna game da sabbin ka'idojin hadin gwiwa tsakanin kasashen biyu, wadanda ma'aikatar samar da ci gaba da gudanar da sauye-sauye ta kasar Sin ta fitar. (Saminu)