Babban kamfanin fasaha na Huawei na kasar Sin tare da kasar Afrika ta Kudu sun hada gwiwwa wajen kaddamar da dakunan karatu na yanar gizo domin inganta yaki da jahilci, inda kashi 15% ne na al'ummar kasar gaba daya suke da damar zuwa dakunan karatu na garuruwansu.
Wannan shirin na hadin gwiwwa ne da kamfanin Vodacom na Afrika ta Kudu, sashin ilimi na Afrika ta Kudu da kuma asusun Nelson Mandela.
Wannan dakin kararu na yanar gizo, wani bangaren samun ilimi ne, wanda yake kan na'urar amfani na zamani mallakar kamfanin Huawei dake cibiyar samar da bayanai da fasahar sadarwar dake sassa da dama a cikin kasar.
Wadannan na'urorin sadarwa guda 400 da Huawei ta samar, an saka mashi dukkan bayanai na litattafan ta yanar gizo da suka hada da adabin Afrika, tarihi, ilimin kasuwanci da dai sauransu. (Fatimah)