Kasashen Sudan da Sudan ta Kudu sun amince a ranar Talata kan gabatar da batutuwan zarge zargen da suke kaiwa junansu na marawa kungiyoyi masu rike da makamai gaban wani kwamitin hadin gwiwa na tsakanin kasashen biyu. Ministan harkokin wajen kasar Sudan Ali Karti da takwaransa na kasar Sudan da Kudu, Barnaba Banjamin sun gana tsakaninsu a ranar Talata a birnin Khartoum, tare da tattauna kan aiwatar yarjejeniyoyin da kasashen biyu suka cimma.
Muna da wani tsarin hadin gwiwa domin warware wadannan matsaloli, in ji mista Karti a yayin wani taron manema labarai na hadin gwiwa tare da mista Banjamin. Mun cimma ra'ayin cewa, ba da kulawa kan zarge zargen da muke wa juna shi ne amfani da tsarin kwamitin tsaro dake da nauyin kula da wadannan batutuwan, a cewar mista Karti.
A nasa bangare, mista Banjamin ya sake tunatar da niyyar kasarsa ta aiwatar da yarjejeniyar hadin gwiwa da aka cimma tare da Sudan. Gwamnatin Sudan ta sanar a kwanakin baya bayan nan cewa, tana da kwararrun shaidu dake nuna yadda hukumomin Juba suke ci gaba da baiwa kungiyoyin 'yan tawaye tallafi, tare da tunatar da 'yancin Sudan na kare fadin kasarta daga hare haren waje. Da farko dai hukumomin Khartoum sun bukaci hukumomin Juba da su aiwatar da yarjejeniyoyin hadin gwiwa da kasashen biyu suka rattabawa hannu a shekarar 2012, da ke nasaba da batun shata iyaka da layin da ba na soja ba tsakanin kasashen biyu. (Maman Ada)