Shugaban kasar Afrika ta Kudu, Jacob Zuma ya yi gargadi a ranar Alhamis ga shugabannin Afrika da kada su wuce wa'adin mulki biyu na shugabancin kasa.
Da yake wannan kalami a yayin dandalin tattalin arzikin duniya (WEF) na Afrika na shekarar 2015 da ya gudana a birnin Cape Town, mista Zuma ya bayyana wa wakilan mahalarta cewa, kundin tsarin mulki ne ya kamata ya takaita wa'adin mulki na shugaban kasa a Afrika, amma ba daga wasu sauran hanyoyi ba, ya kuma kara bayyana cewa, yana adawa da duk wani yunkurin kawo gyaran fuska ga kundin tsarin mulki bisa manufar kara tsawaita wa'adin mulkin shugaban kasa.
Haka kuma shugaba Zuma ya jaddada cewa, ana adawa da tir da allawadai da juyin mulki a Afrika, kana kuma a nan gaba kungiyar tarayyar Afrika AU za ta kafa wani tsari domin fuskantar wannan matsala.
Mista Zuma ya jaddada bukatar bullo da wata hanya mai karfi ta maida martani a karkashin jagorancin kungiyar tarayyar Afrika AU wajen mai da hankali kan yake yake a nahiyar Afrika.
Matsalolin Afrika 'yan Afrika ne ya kamata su warware su da kansu, in ji shugaban Afrika ta Kudu. (Maman Ada)