Masu kare hakkin dabbobi sun yi allah wadai kan yadda wani maharbi Ba-Amurke ya kashe karkanda a kasar Namibia bayan ya biya dala 350,000.
Ba-Amurken mai suna Corey Knowlton, ya shigo kasar ta Namibia ce a ranar 13 ga watan Mayu tare da rakiyar ma'aikatan gidan talabijin na CNN, inda ya harbe karkandan ta hanyar amfani da wata babbar bindiga a arewacin Namibia.
Maharbin mai shekaru 36 daga jihar Texas ta Amurka ya ce, ko kusa kashe karkanda ba dabi'ar su ba ce, amma hakan wani mataki ne da kasar Namibia ke dauka na kare nau'in dabbobin daga bacewa daga doron kasa.
A watan Janairun shekara da ta gabata ne Kulob din Dallas Safari na Amurka ya karbi jinginar takardar umarnin harbin da ma'aikatar kula da muhalli da yawon shakatawar kasar ta bayar na kashe karkandan (Ibrahim)