Jam'iyyar Swapo dake mulki a kasar Namibiya ta lashe babban zaben kasar da ya gudana a ranar Juma'ar makon kiya.
Hakan ya bai wa 'dan takararta na shugabancin kasa Hage Geingob damar kasancewa sabon zababben shugaban kasar na biyar.
Hukumar gudanar da zaben kasar ECN ce dai ta sanar da sakamakon zaben a jiya Litinin, bayan kammala kididdige kuri'un da al'ummar kasar su sama da miliyan 1 da dubu dari biyu suka kada.
Sakamakon zaben ya nuna cewa, Geingob ya samu yawan kuri'un har 772, 528, kimanin kaso 87 bisa dari na daukacin kuri'un da aka kada. Sai kuma Mr. McHenry Venaani na jam'iyyar DTA, wanda ke biye masa da kuri'u 44, 271, yayin da Hidipo Hamutenya na RDP ya zamo na uku da kuri'u 30,197.
Da yake jawabi bayan bayyana sakamakon, Mr. Geingob ya ce, nasarar da ya samu tamkar wani nauyi ne da ko shakka babu, zai yi iyakacin kokarin saukewa.
Game da zaben kujerun 'yan majalissar kasar kuwa, jam'iyyar Swapo ta samu kuri'u 715,026, wanda hakan ya bata damar lashe kujeru 77 cikin 96 da aka fafata a kan su. Sauran jam'iyyun da suka samu kujerun wakilcin al'ummar kasar sun hada da DTA mai kujeru 5, da RDP mai kujeru 3, sai APP da UDF masu kujeru biyu-biyu.
Wannan ne dai karon farko a nahiyar Afirka, da aka tattara sakamakon zabe ta hanyar amfani da na'urorin lantarki. Ko da yake tsarin ya ci karo da matsalolin jinkiri, na tantance alkaluman kidayar kuri'un.
Ana kuma sa ran gudanar da bikin mika mulki ga sabon zababben shugaban kasar ta Namibiya cikin watan Maris na shekara 2015 dake tafe. (Saminu)