in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugabannin Nijar da Benin sun kai ziyarar aiki a Guinea
2015-01-08 10:31:23 cri

Shugaban kasar Nijar Mahamadou Issoufou da shugaban kasar Benin Boni Yayi sun isa birnin Conakry a ranar Laraba domin kawo goyon bayansu ga kasar Guinea, game da kokarin dake na yaki da annobar cutar Ebola, in ji hukumomin wannan kasa. Shugabannin biyu sun kuma dauki niyyar ci gaban da rangadinsu bayan zangon Conakry, da ya shafi sa'o'i uku, kafin su wuce zuwa kasashen Saliyo da Liberiya dake makwabta da kasar da su ma suke fama da wannan cutar.

Bayan bikin maraba da zuwa da ya gudana a filin jirgin saman kasa da kasa na Conakry, manyan bakin biyu an isa da su zuwa fadar shugaban kasa ta Sekhoutoureah, dake tsakiyar babban birnin kasar Guinea. Wannan ziyara ta shugabannin biyu ta biyo bayan ziyarar shugaban kasar Mauritaniya Mohamed Ould Abdel Aziz a ranar Litinin da ta gabata kafin ya wuce zuwa kasashen Saliyo da Liberiya. Shugaban Mauritaniya, dake kuma shugaban kungiyar tarayyar Afrika (AU) a wannan karon, ya kawo taimakon kudi na dalar Amurka dubu dari hudu ga kasar Guinea bisa tsarin yaki da cutar Ebola. Kasashen Guinea da Mauritaniya, suna kuma shirin bullo da wata hanyar soke takardar visa dake tsakanin kasashen biyu. Kasar Guinea kamar sauran kasashen da ke fama da cutar Ebola, tana samun kulawa da goyon baya daga gamayyar kasa da kasa. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China