in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sabon shugaban tawagar MDD kan Ebola ya isa birnin Accra
2015-01-05 09:51:27 cri

Sabon shugaban tawagar MDD kan ayyukan gaggawa na yaki da cutar Ebola, Ismail Ould Cheikh Ahmed, ya isa birnin Accra na kasar Ghana a ranar Asabar.

Mista Ahmed, dake maye gurbin Anthony Banbury, zai kama aikinsa a wannan makon, a cewar wata sanarwa ta tawagar da aka fitar a ranar Asabar.

Bisa yabawa cigaban da bangarori daban daban suka samu wajen yaki da cutar Ebola, mista Ahmed ya bayyana cewa, duk da haka akwai sauran kalubale da ya kamata a cimma. Wannan matsala ce da ta shafi duniya, muna fuskantar lokaci mai wuya dake gabanmu, amma za mu iya samun nasara, in ji mista Ahmed, kafin ya jaddada cewa, ba mu da wani shiri na matakin B, dole mu ci nasara kan cutar Ebola. Wannan dama ce dake gaban, kuma ba za mu nuna sakaci ba.

A cewar wasu alkaluman baya bayan nan na kungiyar kiwon lafiya ta duniya WHO, mutane 20206 suka kamu ko ake zargin sun kamu da cutar Ebola, kana mutane 7905 suka mutu sakamakon wannan cuta tun farkon barkewarta a yammacin nahiyar Afrika.

Tare da rakiyar jami'in MDD mai kula da yaki da cutar Ebola, David Nabarro, mista Ahmed zai je kasashen Liberiya da Saliyo a wannan makon kafin kuma ya wuce kasar Guinea, domin karfafa muhimman dabarun tawagar MDD kan ayyukan gaggawa na yaki da cutar Ebola, da kuma ganin ayyukan dake gudana wajen yaki da cutar Ebola a wadannan kasashe uku, a cewar wannan sanarwa. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China