An bayyana bude karin bankuna masu zaman kansu a nan kasar Sin, a matsayin wata manuniya, ga aniyar mahukuntan kasar ta fadada gyare-gyare ga tattalin arziki.
Kasar Sin dai ta amince da bude sabbin bankuna masu zaman kansu guda 3 a baya bayan nan, a wani mataki dake zuwa gabar da saurin bunkasuwar tattalin arzikin duniya ke raguwa. Rahotanni sun ce, bankunan sabbi za su karkata ne ga bunkasa kananan masana'antu.
Bugu da kari sauye-sauyen da Sin ke aiwatarwa, na zuwa ne lokacin da sashen kananan masana'antun kasar ke fuskantar karancin kudaden gudanarwa, matakin da kuma ke haifar da koma baya ga ci gaban su.
Kaza lika burin mahukuntan kasar na tabbatar da ci gaban matsakaicin bunkasuwar tattalin arzikin kasar, ya sanya karfafa burin magance matsaloli masu alaka da hakan, ta hanyar zurfafa gyare-gyare, da yiwa tsarin tattalin arziki kwaskwarima, tare da kokarin inganta rayuwar al'ummar kasar. (Saminu)