Shugaban kasar Sudan Omar El-Bashir ya gana a ranar Laraba tare da Thabo Mbeki, shugaban rukunin manyan jami'ai na kungiyar tarayyar Afrika (AU) game da batun Sudan ta Kudu (AUHIP), inda suka tattauna kan dangantakar dake tsakanin Sudan da Sudan ta Kudu, shawarwarin kasa da batun bashin waje na kasar Sudan, in ji kamfanin dillancin labarai na SUNA. Taron ya mai da hankali kan batutuwan dake da nasaba da aiwatar da yarjejeniyar dangantaka da kasashen Sudan da Sudan ta Kudu suka sanya wa hannu, da kuma shawarwari na gaba tsakanin gwamnatin Sudan da 'yan tawayen SPLM dake bangaren arewacin kasar, in ji ministan kasa a fadar shugaban kasa, Al-Rashid Haroun da kamfanin dillancin SUNA ya rawaito.
Ganawar ta kasance wata dama wajen tabo maganar shawarwarin kasa, da kuma yadda za'a janyo kungiyoyin 'yan tawaye shiga shawarwarin, batun yankin Abyei da batun bashin waje na kasar Sudan, in ji mista Haroun tare da bayyana cewa, taron ya tabo maganar sasantawa kan tsaro da yarjejeniyoyin da aka sanya wa hannu tare da Sudan ta Kudu domin tattara kwamitin hadin gwiwa kan batutuwan da suka shafi siyasa da tsaro tun daga wannan watan Nuwamba, domin cimma damar kafa wani yankin da babu sojoji a kan iyakar kasashen biyu, da kuma bude hanyoyin kan iyaka domin saukaka zirga-zirga harkokin kasuwanci da tattalin arziki tsakanin kasashen biyu.
A cikin watan Satumban shekarar 2012 ne, kasashen Sudan da Sudan ta Kudu suka rattaba hannu kan wata yarjejeniyar dangantaka a birnin Addis Abeba na kasar Habasha a karkashin jagorancin tarayyar Afrika (AU). (Maman Ada)