Ofishin jakadancin kasar Sin dake Somaliya a ranar Lahadin nan ya ba da gudunmuwar kudi ga kasar Somaliya har kwatankwacin dalar Amurka 20,000 a kokarin taimakawa wadanda ke fama da fari a sassan kasar.
Jakadan kasar Sin a Somaliya Wei Hongtian wanda ya mika gudunmuwar ga Abdulkader Abdi Farah, sakataren din din din na ofishin firaministan kasar a Mogadishu ya ce, kudin gudunmuwa ce da ma'aikatan ofishin jakadancin suka hada a tsakanin su domin taimakawa 'yan uwansu dake da matukar bukata, yana mai bayanin cewa, a ko da yaushe suna kasar ne domin taimakawa al'ummar Somaliya dai dai karfinsu, don haka yanzun ma manufar wannan gudunmuwa ita ce su mika fatan alheri da goyon baya ga al'ummar Somaliya daga gwamnati da daukacin al'ummar Sinawa.
Da yake karban gudunmuwar, Aldulkader Abdi Farah ya godewa gwamnati da al'ummar kasar Sin bisa ga taimakonsu a kan lokaci, ya kuma jinjinawa kokarin ofishin jakadancin na kara dawo da huldar jakadanci tsakanin kasashen biyu. Ya ce, wannan taimako ya zo ne a daidai lokacin da sama da al'ummar kasar miliyan daya ke bukatar agajin gaggawa na kayayyakin bukata.
Tun da farkon makon da ya shude, babban magatakardar MDD Ban Ki-moon ya yi kira ga kasashen duniya da su ba da agajin gaggawa ga ak'ummar kasar ta Somaliya wadanda suke da matukar bukatar taimako, yana mai bayanin cewa, al'ummar kasar dake zaune a kudancin yankuna za su fuskanci matukar yunwa kamar yadda ya faru a shekara ta 2011. (Fatimah)