Mista Zhao ya ce, koda yake a halin yanzu babu cutar Ebola a Najeriya, amma rigakafi ya fi magani, don haka samar da wadannan na'urori mataki ne na kara inganta shirin kandagarkin yaduwar cutar. Ya ce kamfanin CWAY ya riga ya raba kyautar na'urorin auna zafin jikin dan Adam ga makarantu 1500 a kudancin Najeriya, kuma zai ci gaba da yin hakan a wasu sauran yankunan Najeriya.
Jami'an hukumomin ilimi na birnin Abuja, da na tarayyar kasar sun yabawa kamfanin na CWAY, bisa wannan gagarumar gudummawa da yake bayarwa al'ummar kasar. Daya daga cikinsu, Hajiya Binta Nasir, wadda ke aiki a hukumar kula da ilimi a matakin farko dake Abuja ta bayyana ma wakilinmu ra'ayinta.(Murtala)