Babban manajan kamfanin CWAY reshen birnin na Abuja Mista Zhao Xingang, ya ce kamfaninsa na samun goyon-baya, da taimako kwarai daga al'ummar Najeriya, yayin da yake kokarin bunkasa harkokin sa a kasa, matakin da ya sa ya ga dacewar daukar nauyin taimakawa al'ummar kasar gwargwadon karfinsa.