Firaministan kasar Namibia, kuma 'dan takarar shugabancin kasar a babban zaben dake tafe cikin watan Nuwambar mai zuwa Hage Geingob, ya zargi jami'an da kan sanya ido ga zabuka a nahiyar Afirka da rashin adalci.
Mr. Geingob wanda ke yiwa jam'iyya mai mulkin kasar ta Namibia takara, ya ce, sau da yawa irin wadannan jami'an sa ido na nuna banbanci, tare da fidda bayanan san rai, yayin da suke bayyana sakamakon abin da suka gani a zabuka.
Firamistan Namibian dai na wannan tsokaci ne a jawabinsa na bude taron karawa juna sani da aka shiryawa jami'an 'yan sanda, domin fuskantar kalubalen wanzar da zaman lafiya yayin zabe.
A cewarsa, bisa la'akari da yadda al'ummar kasarsa suka gudanar da zabuka da dama cikin nasara, akwai fatan za a kai ga fara shirya zabukan gaba, ba tare da bukatar sanya idon wasu jami'ai daga ketare ba.
Geingob ya kara da cewa, kamata ya yi jama'ar kasar su zamo alkalai game da sahihancin zaben kasarsu da suka yi fafutukar cimma nasararsa. (Saminu)