A gun taron ministocin kungiyoyin uku da aka kammala a birnin Bujumbura dake kasar Burundi, an sanar da cewa, za a kaddamar da yankin yin ciniki maras shinge na kungiyoyin uku a gun taron koli na kungiyoyin da za a gudanar a watan Disamba na bana a birnin Alkahira dake kasar Masar.
Yankin din yana shafar kasashe 26 na Afirka, yawansu ya kai rabin membobin kungiyar AU, kuma yawan mutanen kasashen ya kai miliyan 625, yawan GDP nasu ya kai dala biliyan 12, wanda ya kai kashi 58 cikin dari na dukkan kasashe membobin kungiyar AU. Yankin zai kasance yanki mafi girma na yin ciniki cikin 'yanci a nahiyar Afirka, kana zai zama muhimmin kashi na yankin yin ciniki maras shinge na daukacin nahiyar Afirka da aka shirya kaddamarwa a shekarar 2017. (Zainab)