Kasar Togo ta kyautata kwarewarta a cikin rahoton ciniki na shekarar 2015, tare da samun maki goma sha biyar idan aka kwatanta da na shekarar 2014 domin kasancewa cikin kasashe goma wadanda suka fi jajircewa wajen kawo sauye-sauye a duniya. Togo ta zo ta 164 a cikin rahoton shekarar 2014 zuwa ta 149 a cikin rahoton shekarar 2015, lamarin da ya baiwa kasar damar kasancewa ta uku a cikin kasashe goma a duniya da suka fi cika alkawuransu na yin sauye-sauye domin kyautata yanayinta na hada hada. Wannan cigaban da kasar Togo ta samu na da nasaba bisa sanya muhimmanci wajen kawo sauye-sauye ta fuskar kafa kamfanoni, ba da kariya ga kananan masu zuba jari, biyan haraji da sauransu. (Maman Ada)