Kasar Togo ta yi bikin cikon shekaru 54 da samun 'yancin kasar a ranar Lahadi, kuma ta shirya wani gagarumin atisayen soja da na farar hula na tsawon sa'o'i uku, tare da samun halartar kungiyar sojojin kida ta rundunar sojojin kasar Ghana a matsayin babbar bakuwar musammun da aka gayyato, bikin kuma da aka shirya a kallacin sabuwar fadar shugaban kasa dake birnin Lome. Shugaban kasar Togo Faure Gnassingbe ne ya kunna wutar samun 'yancin kasar a dandalin samun 'yancin kasar. A cikin jawabinsa zuwa ga al'ummar kasar Togo baki daya, mista Faure Gnassingbe ya gabatar da jadawalin samun cigaban kasar zuwa kashi uku. (Maman Ada)