Shugaba Koroma ya bayyana haka ne a yayin da ya kai ziyarar aiki a cibiyar gudanar da bincike kan wadanda suka kamu da cutar Ebola da dakin gwaje-gwaje na asibitin sada zumuncin kasashen Sin da Saliyo dake karkarar birnin Freetown a wannan rana da safe, ya kuma bayyana cewa, tun barkewar cutar Ebola a kasarsa, kasar Sin ta samar wa kasar taimako na kudade da na kayayyakin agaji, har ma ta tura likitoci zuwa kasar Saliyo, hakan ya sa yana matukar godiya ga kasar Sin.
Ya kara da cewa, yana matukar farin ciki don jin labarin cewar, ministan harkokin wajen kasar Sin Wang Yi ya yi kira ga gamayyar kasa da kasa da su tsayawa tare da Afirka wajen yaki da cutar Ebola, a yayin da yake ba da jawabi a babban taron MDD.
Haka kuma, Mr.Koroma ya yi kira ga ma'aikatan lafiya na kasar Saliyo dake wannan asibiti da su yi koyi da masanan kasar Sin, don kyautata fasahohinsu da abin ya shafa. (Maryam)




