in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin da Saliyo sun tattauna kan zuba jari da hadin gwiwa a tsakaninsu
2014-07-22 16:10:40 cri
A kwanakin baya, mashahurin masanin tattalin arziki na kasar Sin Lin Yifu ya jagoranci tawagar 'yan kasuwa ta kasar Sin da kai ziyara a kasar Saliyo dake yammacin nahiyar Afirka, inda suka yi bincike kan yanayin zuba jari a kasar, haka na kuma shi da wasu jami'an gwamnatin kasar Saliyo sun tattauna kan yiwuwar zuba jari da masana'antun dake bukatar ma'aikata da ayyuka da yawa na kasar Sin za su yi a kasar Saliyo.

Lin Yifu ya bayyana cewa, ana raya tattalin arziki da zamantakewar al'umma a kasar Saliyo yadda ya kamata, 'yan kwadago suna da kwarewa, da kuma yanayin zuba jari ya yi kyau. Ya kara da cewa, burin ziyararsa a wannan karo shi ne neman shirin raya kasar Saliyo don samar da damar zuba jari ga kamfanonin kasar Sin, kuma yana fatan kasashen biyu za su samu moriyar juna ta hanyar hadin gwiwarsu.

Shugaban kasar Saliyo Macky Sall ya gabatar da sabuwar manufar raya tattalin arziki da zamantakewar al'ummar kasar a shekarar 2012, wato shirin raya kasar Saliyo, inda aka tsaida gina kasar don maida kasar a matsayin cibiyar cinikayya ta yankin yammacin nahiyar Afirka, kana kasar za ta kasance sabuwar kasar da ta fi samun ci gaba a duniya a shekarar 2035. Ana sa ran cewa, yawan jarin da za a zuba kan shirin zai zarce dala biliyan 20.

Yawancin 'yan kasuwa na kasar Sin da suka zo kasar Saliyo ziyara a wannan karo su ne wakilan masana'antun masaka da na samar da kayayyakin yau da kullum. Ministan kula da aikin raya tattalin arzikin kasar Saliyo Abdoul Aziz Tall ya nuna kyakkyawar fata ga makomar zuba jari da kamfanonin Sin suka yi a kasar Saliyo.

A matsayin wani aiki daga cikin shirin raya kasar Saliyo, gwamnatin kasar ta kafa wani yankin masana'antu dake Diamniado, wanda ke da kilomita 45 da babban birnin kasar Saliyo, kuma aka gudanar da manufofi masu rangwame a yankin don jawo jarin da kasashen waje suka zuba. Kuma tawagar 'yan kasuwa ta kasar Sin za ta kai ziyara a yankin. Minista Tall ya bayyana cewa, kasar Saliyo tana fatan kamfanonin kasar Sin za su zuba jari a fannoni daban daban a kasar. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China