An bayyana hadin gwiwa tsakanin MDD da ragowar kungiyoyin raya kasa da kasa a matsayin wani muhimmin ginshiki na wanzar da zaman lafiya da tsaro a dukkanin fadin duniya.
Cikin sakon da ya karanta ranar Talata 6 ga wata gaban zauren kwamitin tsaron MDD a madadin kungiyar AU, zaunannen wakilin kasar Habasha a MDD Takeda Alemu, ya yaba da irin kyakkyawar alakar dake tsakanin MDD da ragowar kungiyoyi, da hukumomin kasa da kasa.
Alemu ya ce, duniya ta dade da shaida irin tarin nasarori da aka cimma a fannin wanzar da zaman lafiya da tsaro a sassan duniya daban daban, sakamakon managarcin shirin hadin gwiwa dake wanzuwa tsakanin MDD, da kuma kungiyoyin shiyya-shiyya da na nahiyoyi, wadanda karkakin dokokin MDD, da kuma kudirorin kwamitin tsaron majalissar ke aiki kafada da kafada, wajen cimma burin da aka sanya gaba.
Duk da irin wannan tarin nasarori da, a cewarsa, aka rigaya aka samu, a sa'i guda Alemu, na ganin akwai sauran tarin aiki da ya kamata a sanya gaba, domin dai tabbatar da cimma moriyar juna, da kungiyoyi, dama hukumomin kasa da kasa ka iya samarwa ga ci gaban duniya. (Saminu)