in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin ta ba da tallafi wajen horar da mata dake fama da ciwon kanjamau na kasar Zimbabwe a fagen kiwon kudan zuma
2014-04-29 16:22:39 cri

Iyalai na wadannan mata suna fama da talauci ne, saboda haka ba su iya biyan kudi don samun jinya ba. Amma, fasahohin da suka samu na kiwon kudan zuma sun taimake su wajen haifar da fatan ganin makoma mai kyau kan rayuwarsu. Yanzu, lokacin ya yi da suka samu kudin shiga bisa kokarin da suka yi. Kayayyakin da suka haddada da ruwan zuma, kamar da abin sha, da man shafawa, da sauransu, dukkansu za su taimake su wajen kyautata zaman rayuwarsu.

Jakadan kasar Sin dake kasar Zimbabwe Mista Lin Lin ya bayar da takardun shaidu na kammala karatu ga wadannan mata, inda ya taya musu murnar kwarai, tare kuma da yin godiya ga dukkan ma'aikatan da suke kokarin gudanar da ayyukan kos din. Lin Lin ya ce,

"Muna farin ciki da ba da tallafin kudi na dalar Amurka 6200 kan wannan aikin horo, wannan ya nuna kyakyawan fatan kasar Sin na goyon bayan bunkasuwar aikin gona ta kasar Zimbabwe, da kuma kyautata zaman rayuwarsu, shi ne kuma hakikanin mataki ne da kasar mu ta dauka a wannan fannin. Sinawa su kan ce, koyar wa mutane fasahohin kama kifi ya fi bai wa kifi. Saboda haka, mun yi imanin cewa, koyar wa mutane wasu fasahohi, ciki har da kiwon kudan zuma, hanya ce mafi amfani wajen taimake su kyautata zaman rayuwarsu cikin 'yanci."

Shugabar sashen kula da harkokin siyasa na ofishin jakadancin kasar Sin dake Zimbabwe, madam Liu Dan ta bayyana cewa, matakin da gwamnatin kasar Sin ta dauka na horar da matan da suka kamu da ciwon kanjamau na Zimbabwe wajen samun fasahohin kiwon kudan zuma, shi ne daya daga cikin ayyuka guda uku da aka gudanar da su a kasar din bisa shirin sada zumunta tsakanin jama'ar Sin da kasashen Afrika a shekarar 2013. An tabbatar da shirin nan ne don kyautata zaman rayuwar wadannan mata, da kuma samar da su kudin samun jinya.

"Mun kafa wannan kos ne don horar da mata masu kamu da ciwon kanjamau na lardin Mashonaland ta tsakiya, ban da koyar da su kan fasahohin kiwon kudan zuma, kuma za a samar da asusun raya sana'o'i. Daga watan Nuvwamba na bara, mun soma horar da mata guda 30, mun kuma raba su zuwa wasu kananan kungiyoyi, ko wace kungiya na hade da mutane 5 zuwa 10, dukkan kungiyoyin sun iya neman rancen kudi, don raya sana'arsu. Kudin shiga da za su samu, za a yi amfani da su wajen samun jinya, saboda mutanen da suka kamu da ciwon kanjamau na bukatar cin magani cikin dogon lokaci, amma gwamnatin kasar Zimbabwe ba ta da isassun kudi don ba su tallafi ba. A hannu guda kuma, za a yi amfani da kudin kan zaman rayuwar yau da kullum na iyalan wadannan mata. Yanzu, kiwon kudan zuma ya riga ya zaman muhimmiyar hanya ce ta samu kudin shiga na iyalansu."

Har illa yau dai, madam Liu Dan ta kara da cewa, ban da horar da matan da suka kamu da ciwon kanjamau fasahohin kiwon kudan zuma, kuma an gudanar da sauran ayyukan tallafi guda biyu a kasar Zimbabwe bisa shirin sada zumunta tsakanin jama'ar Sin da kasashen Afrika. Daya daga cikinsu shi ne, taimakawa lardin Masvingo wajen yin shara da gyare-gyare kan madatsar ruwa, daya na daban shi ne samar da kekuna kyauta ga kananan asibitocin dake kauyyuka na lardunan Masvingo, da Manicaland.

Kamar yadda jakada Lin Lin ya bayyana, bisa zurfafa yin cudanya a tsakanin jama'ar Sin da kasashen Afrika, za a kara aiwatar da ayyukan more rayuwar jama'a a nahiyar Afrika, ta yadda za a kawo alheri kai tsaye ga jama'a, tare da kara hada kan jama'ar bangarorin biyu. (Bilkisu)


1 2
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China