in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin ta ba da tallafi wajen horar da mata dake fama da ciwon kanjamau na kasar Zimbabwe a fagen kiwon kudan zuma
2014-04-29 16:22:39 cri


Kasashen dake kudancin Afrika, yanki ne da aka fi fama da ciwon kanjamau a duniya, ciki kuwa hadda kasar Zimbabwe da mutanen masu dauke da kwayoyin cutar suka kai kimanin miliyan 1 da dubu dari 2, sannan galibinsu matasa ne, wadanda suke da kashi 15 cikin dari. A kauyukan kasar dai, iyalai na masu daukar cutar kanjamau da yawa suna fama da talauci sakamakon irin ciwon. Shin ta yaya za a taimaka masu? Yanzu ana gudanar da wani aiki bisa gwaji a kasar ta Zimbabwe, wanda gwamnatin kasar Sin ce ta ba da tallafin kudi wajen aiwatarwa, da nufin taimaka wa wadannan mutanen na musamman.

A ranar 3 ga watan nan na Afrilu a wani kulob dake garin Mvurwi na lardin Mashonaland ta tsakiya, an shirya bikin kammala kos din game da horar da matan dake fama da ciwon kanjamau kan fasahohin kiwon kudan zuma, wannan aiki da aka gudana ne bisa "ayyukan sada zumunta tsakanin jama'ar kasar Sin da na kasashen Afrika" da gwamnatin kasar Sin ta kaddamar a yayin taron ministoci karo na biyar game da dandalin tattaunawar hadin kai tsakanin Sin da kasashen Afrika da aka shirya a shekarar 2012, da nufin goyon baya da inganta gudanar da cudanya da hadin kai tsakanin kungiyoyin jama'a, mata, matasa na bangarorin biyu.

Akwai mata 30 na wurin sun karbi takardun shaida na kammala karatu a yayin bikin, daukacinsu sun fito daga iyalan dake da mutane masu kamu da ciwon kanjamau, kuma yawancinsu na daukar cutar. Horon da aka yi musu na tsawon 'yan watanni ya sanya su samu fasahohin kiwon kudan zuma.

Wannan wakar da muke saurara yanzu ta nuna wa masu sauraro karfin rayuwa, da wuyar ake iya tunanin wakar ta fito ne daga wadannan matan dake kamu da ciwon kanjamau na kasar ta Zimbabwe. Wasu daga cikinsu matasa ne, wasu ma tsoffi ne. Ko da yake sun gamu da rashin sa'a saboda ciwon da suka kama, amma a wannan lokacin da suke rera waka, dukkansu suna jin dadi kuma suna murmushi, saboda sun samu takardun shaida na kammala karatu game da kiwon kudan zuma. Shugabar kulob na National Federation Grass-Roots Women's na kasar Zimbabwe, madam Betty Mfero, wadda ta mika musu takardun shaida, ta bayyana a yayin bikin kammala karatu cewa,

"Kun san mutane da yawa ne ba su son ambatar ciwon kanjamau, mun hada kan wadannan matan dake fama da ciwon kanjamau na wurin, ta yadda hankalinsu ya kwanta yayin da suke fuskantar ciwon. Matsala daya kacal a gabanmu shi ne, rasa isassun kudi. Saboda haka, mun yi mu'amala da ofishin jadakancin kasar Sin dake Zimbabwe, inda suka bayyana cewa, ko da yake ba su da kudi da yawa ba, amma suna son taimake mu. Hakan dai muka fara gudanar da aikinmu na farko a karkashin tallafawar gwamnatin kasar Sin, inda suka gabatar wa matan abinci, wuraren kwana, da samar da kudin sayen akwatin kudan zuma, ta yadda matan suka iya samun saukin koyon fasahohin kiwon kudan zuma. Har illa yau sun baiwa matan garantin kananan rancen kudi, don su raya sana'o'insu a nan gaba."

1 2
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China