Lamarin ya faru ne lokacin da wadanda hadarin ya rusa da su galibin su 'yan Hindu masu ziyarar Ibada ke kan hanyar su ta zuwa wani wurin baje kolin kayayyaki ke kokarin ketare titin layin dogo a tashar jirgin kasan karkarar Dhamara,kimanin kilomita 200 daga Patna babban birnin jihar,inda jirgin da ke sheka gudu ya murkushe su ya kuma halaka mutane 37 nan take kana ya jikkata wasu 70, inda aka kwantar da su a wani asibiti da ke kusa,yayin da wasu kuma suka ji rauni mai tsanani.
Wani jami'in da ya bukaci a boye sunansa ya ce, adadin wadanda suka mutu yana iya karuwa. Kuma jami'an kula da jiragen kasa na kasar Indiya sun bayyana cewa,jirgin da ke sheka gudu, bai rage gudu ba a lokacin da ya doshi tashar,domin ba a tsara cewa jirgin zai tsaya a tashar ba tun farko.(Ibrahim)