in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Roma ta lallasa Cagliari, a wasan share fagen shiga gasar zakarun turai ta gaba
2014-04-09 15:50:16 cri
A ci gaba da buga gasar Serie A ta kasar Italiya, kulaf din Roma ya doke Cagliari da ci 3 da daya. Yayin wasan da kulaflikan biyu suka buga a ranar Lahadin da ta gabata. Wanda kuma hakan ya baiwa Roman damar samun tikitin shiga gasar zakarun turai a kakar wasanni ta badi.

Yanzu dai haka Roma ta haura Fiorentina dake matsayi na 4 a gasar ta Serie A da maki 21, gabanin wasanni 6 na karshe.

Dan wasan Roma Mattia Destro ne dai ya zamo zakaran wasan na karshen mako, bayan da ya ciwa kulaf din sa dukkanin kwallaye Uku. Da farko ya samu nasarar zura kwallon a zaren kungiyar ta Cagliari da tallafin Gervinho ne kafin tafiya hutun rabin lokaci. Sai kuma kwallon sa ta biyu mintuna 12 bayan dawowa daga hutun rabin lokaci. Ya kuma sanya kwallo ta Uku mintuna 17 kafin a tashi daga wasan.

Kafin dai a tashi wasan, sai da dan wasan Cagliari Mauricio Pinilla ya ciwa kulaf din sa kwallo guda. Duk dai da hakan Roma ta yi gaba da makin ta uku, a karon farko da ta samu nasarar lallasa Cagliari a gida tun bayan makamanciyar wannan nasara da ta samu a shekarar 1995.

Yayin da kulaf din Roma ke kara samun tagomashi a wasannin da yake bugawa cikin gasar ta Serie A, shi kuwa kulaf din Napoli tauraruwar sa ce ke disashewa, sakamakon nasarar da Parma ta samu a kansa da ci daya mai ban haushi a wasansu na ranar Lahadi. Wanda kuma hakan ya maida shi kasan Roma da maki 12.

Tuni dai kocin kungiyar ta Napoli Rafa Benitez ya yi amannar cewa, ba zasu iya haura matsayi na uku a gasar ta Serie A ba. Yana mai cewa yayi takaicin yadda reshe ya juye da mujiya a wasansu da Parma, bayan kasancewar 'yan wasan sa ne ke sarrafa wasan daga farko, kafin a zira musu kwallo daya mai ban haushi.

Kocin nan ya ce lallai sun rasa wata dama, ba za su iya kaiwa ga matsayi na biyu ba, duba da yadda Roma ta lashe wasannin da su, suka gaza lashewa. Wannan shi ne gaskiyar lamari, duk da haka za su yi kokarin kare matsayi na uku, su kuma fuskanci zagayen karshe na gasar Coppa Italiya.

Yanzu dai haka Jeventus ne ke kan gaba a gasar ta Serie A da maki 81, sai Roma dake matsayi na biyu da maki 76. Yayin da kuma Napoli ke biye da maki 64 a matsayi na uku.(Saminu Alhassan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China