in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An sake samun aukuwar wani hadari a daya daga filayen wasan kwallon kafan kasar Brazil
2014-03-31 18:05:33 cri
A ranar Asabar din data gabata ne aka sake samun aukuwar wani hadari, a filin wasan kwallon kafa na Etta Gellar dake St Paul na kasar Brazil, filin da aka kusan kammala aikin sa. Daya kuma da filayen da ake fatan za a buga gasar cin kofin kwallon kafa ta duniya dake tafe.

Rahotanni sun ce wani ma'aikaci ya fado daga wani wuri mai tsayin mita 8 yayin da yake aikin sanya kujera. Tuni dai aka riga aka kai wannan ma'aikaci asibiti, sai dai babu wata masaniya kan hakikanin yanayin da yake ciki.

Wannan ma'aikaci na aiki ne a kamfanin Fast dake kula da sanya kujera kadai, yayin da kuma kamfanin Odd Brett ke gudanar da aikin ginin filin wasa.

Ba dai wannan ne karon farko, da za a yi amfani da kujerun da wannan kamfani na Fast ke kafawa a manyan filayen wasanni ba. Inda a baya kamfanin ya sanya kujerun da aka yi amfani da su yayin gasar wasannin motsa jiki ta Olympic a birnin Landan, da filin wasan Salvador dake Brazil da sauransu.

Kokarin gudanar da gasar kwallon kafan duniya bisa bukatar hukumar FIFA ne dai ya haifar da hayar kujerun musamman, domin amfani da su na wucin gadi a wannan filin wasa.

Wannan ne dai karo na Biyu da aka samu aukuwar hadari a wannan filin wasa na Etta Gellar. Inda a karshen watan Nuwambar bara ma, wani karfe ya fado ana tsaka da aiki, nan take kuma ya yi sanadiyyar mutuwar wasu ma'aikata su Biyu. (Fatimah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China