Gwamnatin kasar Sudan ta Kudu, ta zargi 'yan adawa dake goyon bayan korarren mataimakin shugaban kasar Riek Machar, da shirin kaiwa Malakal, helkwatar jihar Upper Nile mai arzikin mai hari.
Kafar yada labarai ta Ashrouq net ta kasar ce ta rawaito kakakin rundunar sojin kasar Philip Aguer, na bayyana hakan a ranar Litinin. Aguer ya ce, dakarun dakewa tsohon mataimakin shugaban kasar biyayya sun isa yankin Dungli, mai tazarar kilomita 8 daga Malakal, a wani mataki da tsagin gwamnatin, ke zargin da shiri na kaddamar da hare-hare nan da dan lokaci. Ya ce, tuni sojojin gwamnati suka shiga shirin ko ta kwana.
Tun dai cikin watan Disambar bara ne sassan biyu, ke ta dauki ba dadi, a wani mataki da mahukuntan kasar ke kallo, a matsayin yunkurin 'yan adawar na kifar da gwamnatin mai ci.
A watan Janairun da ya gabata, bangarorin biyu sun daddale yarjejeniyar tsagaita wuta a birnin Addis Ababan kasar Habasha, sai dai kawo wannan lokaci, suna ci gaba da zargin juna da karya alkawuran da aka zartas. (Saminu)