Dakarun sojojin ruwa na Nigeriya a ranar Laraban nan 6 ga wata suka gargadi 'yan fashin teku da sauran masu aikata miyagun ayyuka kada su shiga yankin kasar ta ruwa.
Babban jami'i mai kula da rundunar gabashin kasar Joe Aikhomu ya ba da wannan gargadi lokacin da yake dudduba kayayyakin aiki a cikin babban jirgin na Pathfinder dake garin Fatakwal, babban birnin jihar Rivers dake kudancin kasar.
Aikhomu ya ce, rundunar sojin ruwan ta karfafa matakan da take dauka don dakile duk wani ayyukan satar mai da fashin teku a cikin duk wani kurdi da kan ruwan kasar.
Duk da kalubalen da ake fuskanta wajen aiwatar da ayyuka, rundunar sojojin ruwan kasar a shirye take ta yaki da 'yan fashin teku da satar mai, in ji jami'in. (Fatimah)