Majalisar dinkin duniya na cigaba da yawaita kokarinta na yaki da matsalar fashin teku dake kamari a wannan yanki na kahon Afrika, musamman ma a kan gabobin kasar Somaliya, bayan ta amince da kebe taimakon kudi na dalar Amurka miliyan biyu domin yaki da wannan annoba.
Wata sanarwa ta cibiyar siyasar MDD kan kasar Somaliya da aka fitar a ranar Alhamis a Nairobi na kasar Kenya ta bayyana cewa, asusun MDD na yaki da matsalar 'yan fashin teku ya amince da wani jerin tsare tsare domin tallafawa ayyukan yaki da 'yan fashin teku a kasar Somaliya da kuma a wasu kasashen da wannan matsala take shafa, hadda ma kasashen Djibouti, Habasha, Kenya, Maldives da Seychelles. (Maman Ada)