Kwamitin masana'antu na majalissar wakilai a Nigeriya ya yaba wa gwamnatin tarayya game da bullo da sabon tsari na kera motoci, wadda ta ce, tsarin zai taimaka wajen inganta sashin kera motoci a kasar.
Majalissar zartarwar kasar kwanan nan ta amince da sabon matakin da zai inganta bangaren kera motoci, sannan kuma ya saka kasar a cikin jerin kasashe masu kera motoci a duniya.
Sai dai kuma da yake bayana lokacin wata ziyara a ma'aikatar masana'antu, ciniki da zuba jari a Abuja a makon da ya gabata, shugaban kwamitin Mohammed Ogoshi Onawo, ya ce, aiwatar da sabon tsarin zai janyo hankalin masu zuba jari a wannan bangaren, tare da ba da kariya ga masu kera ababen hawan, sannan zai kara samar da ayyukan yi.
Ya kara bayanin cewa, kwamitin masana'antu na majalissar wakilan ya goyi bayan harajin da aka dora domin a ba da kariya ga masana'antun kera motoci na cikin gida, sannan a ba su damar inganta amfani da adadin da bangaren zai samar.
Shi ma da yake bayanin lokacin ganawar, ministan masana'antu, ciniki da zuba jari Mr. Olusegun Aganga ya ce, ma'aikatarsa za ta cigaba da hada kai da masu ruwa da tsaki wadanda suka hada da majalissar dokoki wajen aiwatar da shirin da ya shafi masana'antun, yana mai bayanin cewa, sabon tsarin da aka fitar da shi zai kawo saurin cigaba a wannan bangaren, tare da samar da ayyukan yi da kuma arziki a kasar. (Fatimah)